Wednesday, 4 January 2017
aminan juna 101-200
π π π π π π
π π π
π π
π
NaπXarah~B~Bπ
~101-105~
" Ummah mun kusa tafiyar "cewar Zarah, Ummah tace "Au daman da gama exam ko hutawa bazakuyi ba sai tafiya?" "Uhm Ummah wane hutu kuma idan muka je ai mayi acan kinsan hutun bawani yawa ne da shiba fa", ummah tace "ehh hakane, yaushe zaku je ne?" " nan da 2 days insha Allah" Zarah ta bata ansa, " ok Allah ya kaimu" cewar Ummah, Zarah ta ansa da "amin Ummah na".
Amrah ce kwance tana waya da Futha sun dade suna waya sa'annan sukayi sallama tare da shaida mata cewa sun kusa zuwa. Ba qaramin farin ciki Futha tayi ba, saboda yanda take tsananun son ganin Amrah, nan suka kashe wayar kowa na mararin d'an uwanshi.
Washegari!!
Ta kama Friday Amrah ce dasu Mum zaune a parlour, Amra tace " Dad jibi ne muke son tafiyar nan xuwa katsina fa" , Dad yace "Au kice har tym yayi kenan ?", "eh Dad yayi" "ok sai ku fara shirye2 kenan, ko dawa wani abune wanda kuke buqata?", Amtah tace " Eh dad ina so zan masu tsaraba ne" Dad yace "ok kamar nawa kike buqata?", sai da tadanyi tunani kafin tace " dad koma nawa ka bayar zasuyi" ,kudi masu yawa Dad ya zaro a aljihu yabata.
Shirye2 sukeyi ba kama hannun yaro sai kace masu Shirin bari kasar baki daya koni Zarah saida suka bani dariyaπtafiyar da ba wata mai dadewa ba amma sai wannan shiri ake, shiru nayi da bakina na masu fatan sauka lafiya.
Zaune take suna fira da umman ta cikin jin dadi, qarar wayar ta taji tayi saurin dubawa, sunan da tagani yasata daqawa cikin hanzari, "Hello My Amrah ykk?" cewar Zarah dayan bangaran aka ansa da "lfy qlw My Zarah ya umma na?" ta ansa da "lfy qlw take", ok ki gaida ta cewar Amrah" " zataji" "yauwa Zarah na daman inaso ne muje mu ida siyayyar da bamuyi ba saboda time ja qurewa", Zarah tace 'kai my Amrah duk wannan siyayyar da mukayi har sai munyi wata?" "Eh sai anyi ta" qarishe mgnr kamar zatayi kuka, "haba am srry my besty na daina" cewar Zarah "ok to ki shirya gani nan zuwa muje" "sai kin zo amma fa kiyi sauri kafin likacin islamiya yayi", sallama sukayi tare da katse wayar....UrsπZarah~B~Bπ
~106-110~
Zarah bata 6ata tym ba ta shirya tsaf cikin riga da zane yellow nd wyt atamfa , hijab ma wyt tayi kyau sosai, Amrah na zuwa suka wuce, siyayya sukayi mai yawa sa'annan suka koma gd.
Yau ta kama SUNDAY ranar da su Amrah zasu yi tafiya, Amrah ta shirya tsaf cikin riga da skirt blue nd wyt in colour sun mata kyau sosai ta jawo trollyln ta zuwa parlour, "Au har kin shirya tun da wuri haka?" cewar Mum "eh" Mum, "tou kije kiyi breakfast tunda da sauran lokaci" Amrah tace " uhm mum ni na qoshi", kamar ya kin qoshi me kika ci ne? "bakomai cewar Amrah "oya wuce kiyi breakfast" haka dai tayi breakfast din ba don taso ba,
Har gate Mum da Dad sukayi mata rakiya. "To ilyasu dan Allah ku lallaba Allah ya tsare hanya nasanka baka gudu da mota, tou pls kaci gaba da hakan, sannu bata hana zuwa, saidai a dade ba'ajeba inji hausawa, kabi mota a hankali harku isa, Allah ya kaiku lapia" cewar Dad duka suka ansa da "amin" bayan sunyi sallama, Amrah ta shiga mota suka wuce gdn su Zarah.
Ringing biyu ta daga "dafatar kin shirya?" Cewar Amrah, cikin hanzari Zarah tace "eh na shirya ke kadai nake jira" bata rufe baki ba taga Amrah a gabanta tana mata murmushi, Zarah tace " Au kinma iso shine kika kirani, dariya sukayi gaba dayan su sa'annan Amrah taja trollyln Zarah suka fita,
A parlour suka tarar da ummah, nasiha ta masu sosai tare da masu Allah ya kiyaye hanya sukayi sallama har mota ummah ta masu rakiya sa'annan suka wuce wayar Zarah tahau ruri, koda ta duba taga wannan sababbiyar numbern ne dai da ake damunta, barin wayar tayi har ta tsinke bata dauka ba, Amrah tace "Zarah ki dauka mana ana kiranki kina ji", Zarah tace "rabu dani pls! Wlh an dameni da kira ne da number'n nan, ni bana son disturbing wlh", ta buga uban tsaki, Amrah sake da baki tace "Allah ya baki haquri aunty masifan bani na kashe zomon ba rataya aka bani", Zarah tace "naji dai ki qyale ni..." bata gama fadi ba aka kuma kiranta, switch off dib wayar tayi baki daya tana jin haushin wannan anacen dake kiranta kullun duk da ba dauka take ba, a haka har bacci ya daukesu, saboda tafiya daga Sokoto zuwa katsina ba abune me sauqi ba.........UrsπZarah~B~Bπ.
πFatima~Bello~Balaπ.
[12/8/2016, 10:44 PM] zahra bb: [21/03 8:40 AM] Zara Bb: πAMINNAN JUNAπ
ππ π π π
π π π
π π
π
®WHW ®
NaπXarah~B~Bπ
~111-115~
koda suka farka daga bacci har ankusa shiga garin katsina da shigar su Katsina baba ilyasu bai tsaya da su ko ina ba sai Lay out, unguwar su Ammi kenan" horn yayi mai gadi ya bude masu gate, parking yayi sa'annan suka fito,
Jin tsayawar mota yasa Futha fitowa da sauri tunanin ko su Amrah ne, kofar shiga parlour suka ci karo "oyoyo mutanan sokoto sannun ku da zuwa" futha ta fada tana mai farin cikin ganin yar uwar ta.
Anan parlour suka tarar da Ammi itama sannu da zuwa ta hau yimasu, bayan sun huta aka wuce dinning suka ci abinci, anan ne Ammi ke tambayar Amrah mutanan sokoto ta ansa mata da "suna lfy ".
Zaune suke su uku adakin Futha suna ta fira, Futha tace " Amrah shin wannan qawar taki bata mgn ne?"murmushi Zarah tayi wanda ya qara fito da zahirin kyanta, Amrah ce ta bata ansa da " Aa tanayi mana me kika gani?" sai a lokacin zarah tace "meyasa kika ce haka Futha?" "Uhm uhm bakomai kawai dai naga bakice komai ba ne tun zuwanku", dariya sukayi sa'annan suka ci gaba da firar su cikin jin dadi da walwala, wayar Futha ce ta dau ruri ganin aunty NABEELERT ce ke kiranta yasa ta dauka cike da farin ciki tace "hello auntyna" banji me akace ba a dayan 6angaren sai naji tace "Allah sun iso tin dazu ma bara na baki amrar ku gaisa kafin mu zo", bayan sun gaisa da Amrah sukayi sallama tare da tsinke wayar.....UrsπZarah~B~Bπ.
~116-120~
"Haba Farouk meyasa baka jin shawara ne?, yakamata kafi qarfin zuciyar kada ka biye mata ta kai ka gayin nadama a tym din da batada amfani", ajiyar zuciya yayi sa'annan yace "musty kasan fa shi SO baruwan shi da wannan yana zuwa ne a ko ina koda babu son muntun, so baruwanshi da wanda ya dace ko wanda bai dace ayi dashi ba", Musty yace "to naji , amma waya fadama ita ZARAH tana sonka? dahar ka daura wa kanka soyayyar ta haka, haba Farouk ina mai qara baka shawara da kayi hakuri kada kayi sanadin rabuwar way'annan masoya ka tuna fa" AMINNAN JUNA ne" sa'annan........ " Hannun da Farouk ya daga mai yahana shi qarasa mgnr, yace " kaga malam dan Allah ka kyaleni naji da abu daya idan ma zarar bata sona me naka aciki" musty sake da baki yake kallon shi aranshi kuwa ya tausayawa AMRAH dan yasan irin son da takewa Farouk. Baida yanda zayyi da farouk dole ya haqurah ya barshi.
Washegari!!!
Amrah ce zaune akan gado tana tunanin "meyasa Farouk bai kirata ba tun xuwan su katsina?" tin tana hakuri abun har ya fara damunta nd idan ta kirashi wayar bata zuwa, zarah ce ta katse mata tunanin da takeyi tace "my Amrah lfy Kuwa nagan ki haka? Ina kule dake fa duk kin canza tun kafin mu baro sokoto,miye damuwarki haka da har zaki 6oye min ita?"ajiyar zuciya tayi tace "Hmmmm!!! Wlh abun na damuna my zarah tinfa zuwan mu hubby bai kirani ba nd idan na kira bata zuwa, kusan ma ince miki tun kafin mu baro sokoto nake ganin canji a wurinshi, na rasa yanda zanyi dashi, ni damuwa na ma d'aya ne Allah yasa yana lafiya" Zarah tace " amma kuma bana ji kina waya da musty ba jiya?"Amrah tace "ehh wai shima be sani ba ko yana lafiya, munyi dashi zaije ya dubashi a Hostel kin san ya koma can, so kuma shima d'in ina ta nemanshi yaqi picking call d'ina, shi yasa kikaga na damu da yawa" cikin tausayi da jinqan qawarta Zarah tace "kiyi hkr my Amrah may be matsalar network ce, kibari zuwa anjima sai ki qara trying number" haka dai tayi ta bata mgn har ta samu natsuwa.
Shakuwa ce tashiga tsakanin Futha da Zarah kamar sun dade da sanin junan su, ita dai Futha tana jin son zarah aranta nd tana jin dadin zama da ita haka itama zarah take jin son Futha.
"Ammi wai yaushe ne ya AFFAN zai dawo?" ta qarashe maganar cikin shagwa6a, Ammi tace "yakusa dawo insha Allah munyu waya yace baifi kwana biyu ko uku ba ya dawo " Amrah tace "ok Allah ya maidoshi lfy, Ammi kun san fa na dad'e rabona dashi, dan ko a hanya na ganshi ba lallai bane in gane shi nasan shima d'in haka" Ammi tace "injiwa ya fad'a miki? Sai dai idan kexe bazaki ganeshi ba amma shikam dole ya gane ki", ta'be baki Amrah tayi tare da cewa "tou Allah ya dawo dashi lafiya" duka suka amsa da "amin"....... UrsπZarah~B~Bπ.
®WWA®
πFatima~Bello~Balaπ.
[21/03 10:17 PM] Zara Bb: πAMINNAN JUNAπ
ππ π π π
π π π
π π
π
®WHW®
NaπXarah~B~Bπ
~121-125~
BAYAN KWANA BIYU!!!
Yaune ranar da ya affan zai dawo daga uk ya kammala karatun shi na likita.
Shirye2 ne suke tayi a gdn na tarban ya affan basu da kammalawa ba sai 12:00pm kasancewar sai 2 jirgin su zai iso,
Sun shirya tsaf kowanan su yayi kyau sosai sai kace wasu yan uku, ammi ce keta zolayar su suna dariya, anan dai suka wace sai airport, da isar su basu jima ba sai ga jirgin ya iso,
Wani kyakkyawan saurayi ne naga ya fito daga jirgin, fari ne tass shekarun shi baxa su wuce 29 ba, ahankali naga ya nufi gurin da su Futha suke tsaye, da gudu Futha taje ta rungume shi "oyoyo ya affan" fuskar shi dauke da murmushi wanda ke qara fito mashi da kyan shi ya ansa mata da "yauwa lil sis".
Rike da hannun ta har suka iso gurin da su ammi suke cike da girmamawa ya gaida mahaifiyar shi, kamar daga sama yaji su Amrah na fadin "sannu da zuwa ya affan" wanda sai a tym din ya gansu ya ansa da "lfy qlw", ahaka suka kama hanyar zuwa gd......UrsπZarah~B~Bπ.
~125-130~
"Da isar su gd ya affan ya wuce room din shi,bathroom naga ya shiga bai wani jima ba ya fito riqe da towel a hannun shi yana goge ruwan jikin shi, bai wani bata tym ba ya shirya tsaf cikin riga da wando 3Q ya feshe jikin shi da turare yayi kyau sosai, sa'annan ya fito.
A parlour ya same su,"oya tashi muje dinning daman kai kaidai akejira" inji ammi ba musu ya miqe suka wuce dinning, futha ce tayi serving dinsu sa'annan suka fara cin abinci da ka gansu kasan suna cikin jin dadi da walwala "happy family kenan".
Bayan sun kammala parlour suka koma anan fira ta 6arke, shi kuma ya affan sai satar kallon zarah yake yi, kiran sallar la'asar ne ya tada su,dakin su suka wuce don gabatar da sallah, shigar su keda wuya wayar zarah ta dau ruri tana dubawa taga dai wannan sababbiyar number ce da ake damun ta da shi tsaki tayi kana da aje wayar "meyasa bazaki daga ba?" inji futha, nima dai narasa dalilin ta naqin picking din call din nan inji Amrah, kallon ta zarah tayi tace "bakomai kawai dai ban san number bane", Amra tace " bt yakamata ki daga kuda sau daya ne kiji kuma waye ai" Zarah tace "ok naji zan dauka".
Bayan sun kammala sallar ne ya affan ya kira Futha, a dakin shi ta same shi yace "wai lil sis wacece ta tare da Amrah?naga kaman ban santa ba" zarah ce qawar amrah tare suka zo ta bashi ansa, ya akayi ne ya affan?" "no bakomai i just ask kya iya tafiya" tare da bata kayan tsarabar ta harda su amrah sa'annan ta wuce zuwa room dinta.....UrsπZarah~B~Bπ.
NOTE: Plz am very sorry kwana biyu kunji ni shiru bana jin dadin jikina ne shiyasa. Tnx alot. Luv u all my Fansπ
®WWA®
πFatima~Bello~Balaπ.
[12/8/2016, 10:44 PM] zahra bb: [23/03 11:18 PM] Zarah ~ B ~ B: πAMINNAN JUNAπ
π π π π
π π π
π π
π
®WISDOM HAUSA WRITERS®✍π»π.
NaπXarah~B~Bπ
~131-135~
Akwana atashi ba wuya agurin Allah yau su Amrah satin su daya a katsina shakuwa me qarfi ta fara shiga tsakanin zarah da ya AFFAN saboda ta dan fara sakin jikin ta da shi sai dai ba sosai ba, duk da har yanxu bai furta mata yana son ta ba amma su Futha har zolayar ta suke suna cemata matar yaya, tun tana nuna bata so har ta kyale su.
Amrah ce kwance tana ta tunanin abn qaubarta, wayarta ta dau ruri ta sauri ta dauka jin special ring tone data saka mishi, "Haba hubby sai yanxu zaka kirani tun zuwan mu garin nan? Kuma kona kira wayar ka bata shiga", ajiyar zuciya Farouk ya sauke tare da cewa "no my luv bahaka bane wlh", "to yane?" ta fada cikin kunar rai, "banida lfy fa kuma wayana faduwa tayi saida nayi welcome back" ya fada cikin muryar tausayi, "hmmmm!! to meyasa baka kirani koda da wayar musty ce ba? ku bakada number na a kanka ne?" rasa ansar da zai bata yasa yace mata "yanxu dai ba wannan ba plz nd plz am very sorry my luv ki yafe mai kinji" ya fada kamar zaiyi kuka, ajiyar zuciya tayi kana tace "bakomai ya wuce", aranta kuwa wani irin dadi taji daya kirata ga wata soyayyarshi da kullun yake qara mamaye zuciyarta. {Allah sarki soyayya kenan, Allah ya hada mu da masoyan gaskia ba irin su FAROUK ba, ameen ya rabbiππ»},waya suka cigaba dayi kamar batayi fushi da shi ba, ahaka har sukayi sallama tare da tsinke wayar.
Ya AFFAN ne kwance a dakin sa sai juyi yake yi shidai har ga Allah yana son zarah kuma son gaskia yake mata amma ya rasa da yadda zai sanar da ita, ahaka dai har ya yanke shawarar fadawa lil sis dinshi ko zata iya taimaka mashi gurin isar da saqon zuciyar shi,da wannan tunanin har bacci ya dauke shi.
Washegari!!!
Ya affan ne ya kira futha zaune suke suna kallon junan su, ya nisa yace
"lil sis inaso muyi wata mgn dake kinji" Futha tace "ok ina jinka big bro", Affan yace "daman..."sai kuma yayi shiru, dariya Futha tayi don ta gane me yake son fadi tace "daman me ya affan ka fadi mana", "uhm sis kenan Allah ina son zarah amma na rasa ta ina zan fara tun karar ta ne", dariya tayi kana tace " ya affan kenan ai kuwa gara ka fadamata saboda kaga sun kusa tafiya may be ma jibi zasu kuma wlh zarah bata da matsala ina tunanin zata amince dakai".....UrsπZarah~B~Bπ.
~136-140~
" Ido ya zare da gaske kike lil sis"? Tace "Allah da gaske nake ya affan gara ma ka fadamata", Affan yace "to yanxu ya kike ganin za'ayi?" Sai data murmusa sannan tace " Kawai kabari na turo ma ita yanxu dana shiga ciki, amma dan Allah karka kopsa big bruhh" yace "ok sis tnx alot, bazan kopsa miki ba".
Da shigar ta dakin da fara arta ta kalle zarah tace "my cwt Zarah ya affan na kiran ki yana parlour" ido ta xare tace " ni? Ya Affan?" "eh ke fa" Futha ta fada tare da neman wurin zama ta zauna.
A parlourn kuwa ta same shi yana zaune kan kujera a kasa ta zauna "ya affan ina wuni" ta fada cikin girmamawa ya amsa da "lfy qlw ya baqunta?" " Lafiya qlw" tace atakaice, yauwa zarah daman ina... sai kuma yayi shiru ganin shirun yayi yawa yasa yace "yaushe zaku wuce ne?"
Jibi insha Allah ta bashi ansa ok Allah ya kaimu ta ansa da "amin" zaki iya wuce wa, "ok"
Bayan ta wuce kuma duk yaji haushin abunda yayi why why nakasa fadamata,
Zarah ce kwance tana waya da umman ta sun jima suna waya kana sukayi sallama.Alamar shiguwar text taji ganin number ya affan ne yasa ta budewa da sauri ta fara karantawa kamar haka:
"I want to treat you lyk a queen simply bcos you rule my world. I am at ur Service, ur majesty". I really really love u, i hope u luv me too.
Ajiyar zuciya tayi kana ta aza wayar kan kirjin ta, koh dama shine ya affan ke son fadaman ranar da ya kirani? haka ta cigaba da tmbyr kanta, shigowar su Amrah ne yasa ta natsu bt still ta juya mgnr "i really really love u, i hope u luv me too" mgnr Futha ta dawo da ita, wai mekike tunani ne haka inji Amrah, uhm bakomai ta bata ansa..... UrsπZarah~B~Bπ.
®WWA®
®WISDOM HAUSA WRITERS®✍π»π.
πFatima~Bello~Balaπ.
[23/03 11:40 PM] Zarah ~ B ~ B: πAMINAN JUNA π
π π π π π
π π π π
π π π
π π
π
®WISDOM HAUSA WRITERS®✍π»π.
Na π Xarah ~ B ~ B π
~ 141-145~
A daren ranar haka Zarah ta kwana da tunanin Affan, amma kuma ta kasa mishi reply da ta amince, a bangarenshi shima tunanin shi bai wuce qila Zarah bata karbi soyayyarshi ba, haka ya kwana kamar wani zautacce dan son da yakewa Zarah bai misaltuwa, dis is his first time daya fara soyayya, shi yasa yake jinta a jinin jikinshi.
Washe gari tunda safe Zarah ta tashi kamar yanda ya saba ta shiga kitchen, bata tsaya jiran su Futa da Amrah ba ta hau hada masu breakfast n haka Zarah take bata da ganda ko kadan, komai yawan aiki ita baya bata haushi.
Bayan ta gama ta jera komai akan dining table ta shiga ta kira kowa kamar yanda ta saba amma sai ta samu kanta da kasa kira Affan, har sun zauna mum tace "wai ina Affan ne? Hala nawar tashi ce daya saba? Dan na tavvatarda Zarah ta fada mashi tunda kullun saita fada mashi", Zarah sai qwalo ido take sai ji tayi ance "kamar kin sani kuwa mum, ta riga fada min akan kowa, na tsaya yin wanka ne", kyakkywar ajiyar zuciya Zarah ta sauke tare da sinne kanta qasa, koda suka hada ido ya qifta mata qwara daya har cikin ranta taji, taga kuma zahirin soyayyarta a idon Affan, da wannan tunanin suka kammala kalaci itakam kadan taci bada yawa ba.
~146-150~
Bayan sun gama komai na gida Futha tace "yau muke resuming a skul fa kuma ya kamata inje, kunga saiku takani muje tare daga nan har kuga yanda skul din mu take", Amrah tace "aikam haka ya dace, sai mu dora girki da wuri yanda zamu gama da wuri", Futha tace "ai da yake ma yau baba Rabi zata dawo, nasan da wuri zata zo", Amrah tace "hakane kuma, wai qawa yau ya akayine kikayi shiru?" Budar bakin futha cikin sauri tace "she is in love fa" suka dauki shewa harda tafawa, zarah dai batace masu komai ba dan tasan gaskiya suka fad'a, sai can kuma tace "ai qawa da yake kin samu baki dole kimun iskancin da kikeso, dan kin samu Farouk ya kiraki ne fa", wayar Amrah ta dauki ruri da farin ciki tace "kinga dan halak, bawan Allah ana cikin gulmarshi sai gashi ya kira, wama yasan ko jikinshi ne ya bashi", daukan kiran tayi tace "hubby how fa?" Bai bata ansa ba sai yace "dear pls idan kina kusa da Zarah ki bata, ina son gaisawa da ita", cikin kishi Amrah tace "shine kuma bazaka karva gaisuwata ba ko", haquri ya bata nan da nan ta haqura saboda bata sin laifinshi, ta miqawa Zarah wayar, Zarah tace "lapia?" Amrah ta mayar mata da "I dont know, just take d phone kedai zaku gaisa ne I thinks", kar'bar wayar tayi tace "na Amrah ya kake?" Sai daya sauke ajiyar xuciya alaman missing d'inta tukuna yace "lafiya kalao, wai me yasa baki damu dani bane Zarah? Me yasa bazaki dauke ni kamar yanda Amrah ta daukeni ba?" Mamaki sosai maganarshi ta bata tace "ban gane ba", saurin kawar da maganar yayi yace "barshi kawai dear, xan kiraki anjima amma pls karki daga kiran a gaban Amrah", "tou" kawai tace tare da miqawa Amrah wayarya, koda ta kara a kunne taji har ya kashe, abn ya bata haushi sosai amma sai ta kawar dan bata so qawarta ta fahimci tana kishinta ne.
®WISDOM HAUSA WRITERS®✍π½π.
π Fatima ~ Bello ~ Bala π
[12/8/2016, 10:44 PM] zahra bb: πAMINNAN JUNAπ
π π π π π π
π π π π
π π π
π π
π
®WISDOM HAUSA WRITERS®✍π»π.
NaπXarah~B~Bπ
~151-155~
"BAYAN KWANA BIYU"
Abubuwa da dama sun faru daga ciki harda amincewar soyayyar ya Affan da zarah tayi, tun daga tym din soyayya mai qarfi da shaquwa suka shiga tsakanin ZARAH DA YA AFFAN, ammi kuwa tafi kowa jin dadin faruwar hakan sbd ta yaba da hankali da natsuwar ZARAH
Su Amrah na hango sun shirya tsaf kowanan su yayi kyau bama kamar zarah ba, wayar zarah ce ta dau ruri ganin ya Affan ne yasa ta yin murmushin da ke qara fitar da kyan ta "Assalamu Alaikum", naji ta fada, adayan bangaran aka ansa da "wa'alaikun salam y kk tauraruwata?" ta ansa da "lafiya qlw nd u?" "D same" yabata ansa a taikaice", " idan kun shirya ku fito muje ina parking area" "ok gamunan fitowa "tou sai kun fito" tare da tsinke wayar"
"My futha ya Affan yace fa mukadai yake jira" zarah ta fada, dariya sukayi sa'annan sukace "tou matar yaya" tare da fita daga dakin, a palour suka same ammi tana kallo a TV, "ammi zamu tafi fa" inji Futha, "au kuce har kun shirya ma" "eh ammi mun shirya", "ok Allah ya kiyaye hanya ku gaida NABEELERT din" "zataji Amii" tare da yimata sallama suka wuce, a parking space suka tarar da ya affan bayan sun gaida shi suka shiga mota zarah zata shiga baya ya affan ya harare ta "ohhhhh kuce na zama driver dinku kenan", "uhm aa" ta fada "tou oya shiga gaba mu wuce" "ok" sa'annan ta shiga su Futha kuwa ba abunda sukeyi inba dariya bt basu bari ta fito ba.
Haka suka dau hanya sai GRA unguwar su aunty BEELERT kenan, anan ya barsu tare da shaida masu da cewa anjima zai zo ya dauke su, daganan ya wuce.....UrsπZarah~B~Bπ.
~156-160~
A parlour suka same ta kwance kan 3 seater tana kallo mbc bollywood da fara arta ta tarbesu bayan sun zauna ne take cewa "ni nayi fushi kwanan ku nawa a garin nan sai yanxu zaku zo?,, "aunty beelert plz we are sorry wlh muna son zuwa kin san komai sai Allah yasa" Amrah ta fada, " ai yanxu gashi munzo ko?" inji Futha "ni yiman shiru daman nasan kece kika hana su zuwa dan daman kema ba son zumuncin ne Dake ba", "aa fa aunty nifa ba ruwana" tana wata dariya can kasa2, " Amrah wacece wannan bangane ta ba" futha tai carab tace "zarah ce qawar amrah tare suka zo kuma........ " kallonda zarah ta mata ne yasa takasa qarasawa, "kuma me?" inji aunty beelert, "no aunty zan fadamiki bt ba yanxu ba" ta qarashe mgnr cikin zolaya, sun jima suna fira kiran sallar azahar ne ya tada su, bayan sun qare sallah ne wayar zarah ta dau ruri tana dubawa taga dai wannan sababbiyar number ce da ake damunta da shi saidai yanxu ta san mai number ba kuwa bane illah FAROUK har ta tsinke bata daga ba qara kira akayi ganin batada niyar dagawa yasa amrah daga wayar "ajiyar zuciya ya farayi kana yace "haba my zarah meyasa bakya son daga wayana? Kiyarda dani plz wlh zarah INA SONKI son da ban tabayiwa wata ya'mace ba, duk wata soyayya da nakewa Amrah wlh duk shirme ce, kece madubin dubawa na", jin batayi mgn ba yasa shi cewa "talk plz zarah" Amrah da tun da taji muryar hubbin ta ne tayi mutuwar zaune tuni hawaye suka wanke mata fuska ta kasa fadin komai sai rawar jiki da takeyi.........UrsπZarah~B~Bπ
πLUV U ALL MY SWEET SWEET FANSπ.
Note: pls kuyi haquri na rashin jina kwana biyu, hakan ya faru ne kasantuwar biki da mukayi,,,,,,,,,, kuci gaba da kasancewa da Zarah domin jin ci gaban labarin AMINAN JUNA.....
®WISDOM HAUSA WRITERS AND WORLD WRITERS ASSOCIATION®✍π»π.
πFatima~Bello~Balaπ.
[12/8/2016, 10:44 PM] zahra bb: πAMINNAN JUNAπ
π π π π π π
π π π π
π π π
π π
π
®WISDOM HAUSA WRITERS®✍π»π.
NaπXarah~B~Bπ.
~161-165~
Faduwar wayar da sukaji ne ya maida hankalin su gare ta, da sauri zarah ta nufI gurin da amrah take jikin ta sai rawa yake yi, ganin zarah zata taba ta yasa da k'ar ta iya cewa "kada ki tabani macuciya, azzaluma maci amana" sai kuma ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi, tsaye zarah tayi ganin halin da aminiyar ta ke ciki fuskar ta cike da damuwa, a ranta kuwa tana tunanin wace irin mgn ce FAROUK ya fada tunda shi a tunanin shi itace ta daga wayar, muryar amrah ce ta katse mata tunanin da takeyi tana fadin "kin cuceni kin ci amanata zarah, sakayyar da zaki min kenan? daman hausawa sunce tsintatciyar mage bata mage duk abunda namaki a rayuwa da wannan zaki sakaman?," zarah da tunda amrah ta fara mgn hawaye ke ambaliya a fuskar ta tare da girgiza mata kai amma sam amrah taqi ta saurare zarah" futha ce tayi karfin halin cewa "wai meke faruwa ne Amrah? kun barmu a duhu fa" cikin dasasshiyar muryar ta tace "futha yanxu zarah ta rasa wanda zata cuta sai ni, meyasa tun farko bata fadaman SON SHI take ba? meyasa zarah zata man haka? meyasa take son ta tarwasaman rayuwa? meyasa.............. "futha ce ta katse ta da fadin "wa'annan tmbayoyin naki banida ansar su, me tamaki ne? sa'annan wanene take so?" janjayen idanuwan ta tadago tana kallon ta tace "yanxu ta rasa da wanda zatayi soyayya sai hubby na, Farouk wanda nake burin in aura, ashe daman dalilin da yasa ya chanza man kenan a lokaci daya", "watπ³?" Inji futha..... UrsπZarah~B~Bπ.
~166-170~
"A'a amrah impossible, hakan bazata taba faruwa ba, kada kiyi saurin yanke mata hukunci batare da kinyi bincike ba nd duk da kinki fadaman me FAROUK yace a waya nasan ba laifin zarah aciki, kada soyayya ta rufe maki ido ki aikata abunda zakiyi nadama a gaba, kada ki manta zarah nada wanda take su kuma take muradin aure nd......" hannun da ta daga matane yahana ta karasawa "dalla malama ki man shiru bana buqatar jin komai, ke kuma" tare da nuna zarah "daga yau bani ba ke, kar ki kuma nuna kin sanni tunda ke matsiyaciya ce, hmmm.....banga laifinki ba Zarah, laifina ne ai da tun farko na nuna miki soyayya fiye da kaina" Ta inda amrah ke shiga batanan take fita ba duk yadda zarah taso ta saurare ta kin yadda tayi kuka sosai zarah keyi[ni kaina saida na tausaya mata πͺ]
Ranar yadda zarah taga rana haka taga dare sam bacci kin zuwa yayi hakan yasa taje toilet ta dauro alwala ta fara nafila wanda ita kanta batasan adadin ku raka nawa tayi ba, bayan tayi sallar asuba ne ta fara hada kayan ta, cikin sa'a kuwa koda ta fito parlour kofar abude take kasancewar ya affan ya je masallaci, haka ta samu ta fita daga gdn ba wanda ya ganta, tafiya takeyi ba dan tasan inda ta nufa ba haka har gari ya waye keke napep ta samu tace ya kaita tasha.....UrsπZarah~B~Bπ.
®WISDOM HAUSA WRITERS®✍π»π.
πFatima~Bello~Balaπ.
[12/8/2016, 10:44 PM] zahra bb: πAMINNAN JUNAπ
π π π π π π
π π π π
π π π
π π
π
®WISDOM HAUSA WRITERS®✍π»π.
NaπXarah~B~Bπ.
~171-175~
Koda suka isa tasha ba mutane dayawa kasancewar da safe ne, sai zuwa 8 aka fara lodi, tana tunanin kudin motar da zai kaita sokoto, can ta tuna da kudin da ummanta ta bata lokacin da zasu tafi katsina, bayan anqare lodi ne suka kama hanyar sokoto, kallo daya kama zarah kasan tana cikin damuwa.
A bangaren su amrah kuwa, bayan sun tashi basu ganta ba ita amrah ko ajikin ta kasancewar wata tsanar zarah takeji, futha ce ta shiga duba ta har toilet amma wayam ba kowa, a parlour ta tarar da ammi a rikice ta fada jikin ammi, ganin yanayin futha ne yasa ammi cewa " futha lfy naganki haka? , "ammi wlh bamuga zarah ba koda muka tashi ammi kuma duk na duba batanan harda kayanta bangani ba", "innalillah wa'inna'ilaihir raji'un" ammi ta fada "to me aka mata ne wanda zaisa tabar gdn ba tare da bankwana ba?", futha tace " ammi daman jiyane suka samu missunderstanding da amrah", nan dai futha ta fadama ammi duk abinda ya faru, fada sosai ammi tawa Amrah, hakama ya Affan kamar tabbabbe ya zama da yaji zarah bata gdn, ya Affan yayita kiran wayar zarah amma switch off, hankalin shi yayi matuqar tashi har gdn aunty beelert yaje amma Zarah bata can, haka ya dawo jiki ba sukuni, a ranshi yana tunanin ko sokoto taje, da wannan tunanin har baccin wahala yayi gaba shi........UrsπZarah~B~Bπ.
~176-180~
"Assalamu Alaikum" "wa'alaikun salam..., aaaaaaa mutanan katsina sannun ku da zuwa maraba daku, ya hanya?" " lfy qlw umma" zarah ta ansa a taikaice ummah sake da baki tace " lafiya kuwa naganki haka ina amrah ne? "umma............ "Sai kuma ta fashe da kuka mai ban tausayi, "wai me akayi ne kike kuka? wani abunne yasami Amrah?" kai kawai ta gyadamata alamar a'a "to meya faru?" tare da janta zuwa daki, bayan ta rarrasheta ne tace ta tashi taje tayi wanka taci abinci sa'annan suyi mgn, "tou" kawai zarah ta iya fada tare ta mikewa, bataji ma ba ta fito bayan ta shirya, a parlour ta same ummah bayan taci abinci ne cikin natsuwa ummah ke mata mgn "zarah kinatsu ki fadaman meya faru? meyasa baku dawo tare da amrah ba"? cikin dasasshiyar muryarta ta fadama ummah komai da yadda ta baro gdn har ma soyayyar su da ya Affan bata 6oyemata ba kasancewar zarah yarinyace ba mai boyema mahaifiyar ta abu bace, ummah ta tausayawa yartata, haka ummah tayi ta ba zarah mgn tare dayi mata nasiha har taji ta natsu
Ya Affan ne zaune a tsakar dakinsa yayi uban tagumi duk ya rame yayi baqi ya lula duniyar tunani, Futha ce takatse masa tunanin shi ta hanyar dafashi da tayi "ya Affan plz kadaina wannan damuwar ka dubi fa yadda ka koma cikin qanqanan lokaci" cikin rashin son maganar yace " sister kenan dole indamu mana zarah ta kashe wayar ta, kuma banida tabbacin sokoto ta tafi fa, gaskia ni sister gobe zanje sokoto can inda Mum din amrah infadamata abinda ke faruwa dan nasan amrah bata fadamata ba, daganan anuna man gdn su zarah, ko ya kika gani?" " ehh bruhh, kuma wannan ma dabarah ce, Allah yasa adace, amma ka shawarci ammi kaji tata shawarar", "ok haka za'ayi insha Allah, amma ni ina mamakin amrah wlh saboda koni da bamu wani jima da zarah ba akwai abunda bazan taba yarda zatayi shi ba, ina gujema amrah ranarda zata gane gaskia saboda yanxu soyayya tariga ta rufemata ido", cikin qosawa Affan yace "uhm Allah yasa ta gane gaskiya, amma kam Amrah tayi butulci, ta ha'inci zaman tare, sai kice dai ba AMINNAN JUNA ba? A yanda naji labarinsu fa tun suna yara suke tare, aikuwa yaci ace sun fahimci junansu, su gane abnda ko wacensu zata iya yi.........UrsπZarah~B~Bπ.
®WISDOM HAUSA WRITERS®✍π»π.
πFatima~Bello~Balaπ.
[12/8/2016, 10:44 PM] zahra bb: πAMINNAN JUNAπ
π π π π π π
π π π π
π π π
π π
π
®WISDOM HAUSA WRITERS®✍πΌπ.
NaπXarah~B~Bπ
~ 181-185~
Futha tace "amin yaya, amma kam gaskiya Amrah na cikin rudin soyayya kuma......", bata qarasa maganar ba taji Amrah na fadin "sannu magulmaciya, wato gulmata kika kawo gurin yaa Affan ko? Tou wlh koma me zaku fada sai dai ku fada, nace babu ni babu Zarah, na yanke duk wata alaqa dake tsakanin mu, kuma ma da kike fad'in haka, shin wai ni na kori Zarah ne? A gabanki fa akayi komai, ban koreta ba ita ta kori kanta", Futha ranta bace tace "amma ko baki furta kora ba ai kin furta me kama da haka, kin mata gori Amrah, wanda ya kamata ace kinfi qarfin nan, an daina yayin gori fa, an barwa qananan yara, ke kuma yanzu kin wuce minzalin qananan yara", cikin masifa Amrah tace "well! Ki fadi duk abnda kike so Futha, nasan a gidanku nake dole na dauki duk wata baqar maganar...", saukar marin da taji ne ya hana ta qaraaasa maganar da take, yaa affan ne ya mareta ta dafe kumcinta, bata ankara ba ta qara jin saukar wani marin, ba shiri ta fadi qasa tana kuka kamar ranta zai fita........πUrs Zarah~B~Bπ
~186-190~
Da sauri ammi ta fito jin sautin kuka na tashi, cin burki tayi a lokacin da taga amrah kwance a qasa shame shame tana kuka, da hanzari ta isa inda Amrah take, ta dafata tace "daughter! Me ya sameki kike kuka?", Amrah ido rufe ko kallon ammi batayi ba, ganin bata da niyyar bata ansa ne yasa tace "kai Affan me kayiwa Amrah? Futha meke faruwa ne? Answer me mana, am asking youh, tell me what happened with my daughter?", kasa bata ansa sukayi su duka, sun dauki kamar munti 15 a haka, ganin ammi na kuka hawayen ta na ta fita yasa Affan gurfanawa a gabanta, ya dafa kafadarta yace "ammi kuka kike? Me ya saka ki kuka? Rabo na da ganin kukanki tun rasuwar abbah, pls kiyi haquri", sai a lokacin ammi tace "ba dole nayi kuka ba Affan, nayi nayi daku kunqi fada mun abnda yake faruwa, ga yarinya nata faman kuka kuma nasan kun san komai", cikin rashin son fada mata yace "Ammi lafi na ne, nine na mareta" nan ya kwashe komai daya faru ya fada ma ammi, yasha fada sosai shida futha, da qyar ta samu ta rarrashi Amrah tayi shiru amma da sharadi, wai dole sai ta koma Sokoto gobe, ammi tace babu komai tare ma zasu tafi daga nan har su bincika labarin Zarah, ranar haka suka kwana kowa cikin takaici, ita Amrah babban haushinta ma idan ta kira Farouk baya dauka, daga qarshe ma sai yayi off na layinshi.............πUrs Zarah~B~Bπ
®WISDOM HAUSA WRITERS®✍πΌπ.
πFatima~Bello~Balaπ.
[12/8/2016, 10:44 PM] zahra bb: πAMINNAN JUNAπ
πππππππ
πππππ
ππππ
πππ
ππ
π
®WISDOM HAUSA WRITERS®
✍πΌπ✍πΌ
NaπXarah~B~Bπ
~191-195~
Washe gari tun safe suka hau hada kayan zuwa Sokoto banda Amrah da tayi jugum duk ta fita hayyacinta, Futha kam ta fita batunta dan ba kadan take tsananin jin haushin Amrah ba.
Jin shiru har sun fito parlour amma babu amrah yasa ammi ta shiga dakinsu, ta sameta kamar mahaukaciya sai sabbatu take ita daya tana fadin "ni Zarah! Ni kikaiwa kwacen saurayi? Hubby na wanda nake burin aure, yake kiranki da swty, kin cuce ni, bazan taba yafe miki ba a cikin babin soyayya".
Ammi taita magana amma shiru bata ma san tanayi ba, saida ta tafa hannu da qarfi sannan ta zabura hawaye nabi mata kumatu tace "na'am ammi, ina kwana?".
"Ba wannan ba, me kike da har yanxu baki shirya ba? Kuma kin san ke muke jira",
Cikin kalar tausayi tace "ammi ai ban ma san har garin ya waye ba, tunda nayi sallah nake anan, barin hada kayan yanxu dama komai a shirye yake", Ammi tace "tou barin turo futha sai ta tayaki harhadawa", "noo ki barshi ammi ai daman duk a hade suke, gyrane kawai zanyi nasan yanxu zan gama" tayi saurin fadi.
Cikin qanqanin lokaci amrah ta hada komai nata, da qyar take jan trolly dinta ta fito dashi parlour, ta samu Ammi, futha da yaa affan zaune kowa yayi tagumi, kowan su da abnda yake tunani a ranshi, miqewa ammi tayi lokacinda Amrah ta fito tace "Affan karbi akwatinta ka kai a mota", cikin rashin kuzari ya karba ba tare da yace mata uffan ba, bin bayanshi sukayi ya bude masu motar futha a gaba sai Ammi da amrah a baya..........πUrs Zarah~B~Bπ
~ 196-200~
Tafiya suke cikin natsuwa babu gudu dan ammi bata son ana gudu da ita a mota, qarfe 1:40 suka isa babban birnin Sokoto. Basu zarce ko ina ba sai gidansu Amrah.
"Ahh lale marhaban da mutanen katsina, tafiya haka babu sanarwa, sannunku sannku", momy ce ke fadin haka fuskarta sake tare da faraa.
Ammi tace "wlh kuwa maman Amrah, yauwa yauwa, mun sameku lafiya?"
"Lafiya lau ya hanya?"
"Alhamdulillah" Ammi ta fada.
Bayan sun samu natsuwa sunci abinci sunci, Amrah ta koma daki taci gaba da jimami. Futha kuwa qaramin parlour ta koma ta kunna kallo. Yaa Affan ya tafi masallaci sallar jumu'ah dan a ranar jumu'ah ne.
Ya rage saura Ammi da momy kawai a dakin. Ammi tace "nasan zakiyi mamakin ganin mu kwatsam ba tare da kun san da zuwan mu ba"
Momy tace "gaskiya ne, wannan xuwan bazatar ya daure min kai",
Ammi ta nisa tukuna tace "wata 'yar matsala ce ke tafe damu, inda kin kula zakiga yanda Amrah ta canza duk babu walwala a tare da ita",
"Ehh na kula da haka kam, me yake faruwa ne?"
Nan Ammi ta kwashe duk abnda ta sani tun farko har qarshe ta fadwa momy, harda tafiyarda Zarah tayi ma ta fada mata.
"INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN" kawai momy ke fadi, "tou ai ammi bamuga ta zamaba, dole a bincika Zarah idan gida ta dawo, Allah dai ya rufa mana asiri yasa tana gida",
Ammi tace "amin".
Sallamar yaa affan ce ta katse masu zancen da suke, momy tace Affan ko kai zaka kaimu gidansu Zarah? Sai na ringa gwada maka hanya tunda babu nisa ma daga nan, wlh drivern mu yayi tafiya ne, dady kuma yana office bai dawo ba".
Dad'I sosai Affan yaji dan an ambaci Zarah, rabonshi da samun natsuwa yau kwana uku kenan tun barin Zarah katsina.
"Muje momy a shirye nake", ya fada tare da fita daga dakin. Caraf futha ta fito tace "dan allah aje dani ammi", Ammi tace "ya za'ayi a tafi dake bayan kuma ga yar uwarki? Ki zauna ki jira mu bazamu dade ba, kedai kiyi mana fatan samun nasarah kawai".
Momy tace "aahh baza'ayi haka ba, jeki sako hijabinki mu tafi, itma Amrah ai ba wani ya hanata ba",
Kaman daga sama sukaji Amrah tace "Allah ma ya kyauta min inje gidansu maciyya amana, ni wlh ko sunanta ma bana son jin an ambata".
Ammi tace "rufewa mutane baki daallah can", a fusace ta fita tabi bayan yaa affan dake tsaye bakin mota yana jiransu.........UrsπZarah~B~Bπ.
®WISDOM HAUSA WRITERS®
✍πΌπ✍πΌ
πFatima~Bello~Balaπ.
Thursday, 8 December 2016
AMINAN JUNA
Na💕Xarah~B~B💕
~91-95~
Futha! Futha!! Futha!!! Wai kina ina ne haka inata kiranki, Na'am Ammi gani nan zuwa, a parlour tasame Ammi na kallo a TV ta zauna akasa kusa da ita tace Ammi gani, ina kika shige ne inata kwala maki kira bt baki jiba, Wlh Ammi bana kusa ne cewar Futha, ok daman Amrah ce tace takira wayar ki bata shiga, tace na maki albishir nan da 2 days zasu zo itada qawar ta,
Futha ta dago kanta da sauri cikin farin ciki, Ammi yaushe ta kiraki? yanxun nan tace ma anan zasu yi hutun su, sai ki fara shirye2 tarbar su, ok Ammi ta fada tare da tashi zuwa room dinta.
Amrah da Futha yan sa'ane shekarun su zasu zo daya, Futha itace diyar Ammi Watau qanwar dadyn Amrah ita ke bimashi su biyu ne kacal ga iyayen su,
Transfer da akayiwa Abban su Futha ne a wurin aikin su, ya maida su zama a katsina, duk da tym din da zasu dawo Ammi bata ji dadi ba, ba don kome ba sai don nesan da zatayi ne da dan uwanta, saida dady yayi ta bata baki tare da yimata alqawari duk lokacin da yasamu chance zai rinqa zuwa.
Ya'yan su uku ita da mijin ta Namiji daya macce biyu, Usman wanda sukafi kira da "Affan" sai Nabeelert itama tayi aure sai autar su Futha, kasancewar batayi karatu mai tsawo ba tayi aure nd kuma ta riga dadyn Amrah yin aure saboda krtn da yayi mai tsawo kuma Allah bai basu haihuwa da wuri ba shida Mum din Amrah...... Urs💕Zarah~B~B💕.
~95-100~
Alhamdulillah yaune su Zarah da Amrah suka kammala exams dinsu cikin jin dadi da farin ciki, can na hango su suna sallama da course mate dinsu kasancewar yau zasu tafi hutu, bayan sun qare ne naga sun nufi motar su.
Da shigarsu Amrah tasa kiran Farouk bayan ya daga wayar naji tace kana inane yanxu? Ina hostel cewar Farouk, ok ka fito gamu nan zuwa, yace ok sai kun iso,
Hanyar hostel naga sun dusa, a qarqashin wata bishiya tayi parking sa'annan ta sheda ma Farouk cewa sun iso, kafin yazo ne Zarah ta kuma seat din baya ta zauna, saiga Farouk ya iso, da isowar shi ya shiga mota ya zauna "ya exams my luv? exams Alhmdllh, hubby ya taku exams din? da godiya cewar Farouk,to Allah ya taimaka yabamu sa'a da rabu baki dayan mu, duka suka ansa da"amin" da yake su Farouk basu ida tasu ba.
Anan dai sukayi mgnr da zasuyi har take fada mashi cewa nan da 2 days zasu je katsina, Haba my luv yanxu tafiya zakiyi ki barni? No hubby bahaka bane gun qanwar dady zanje fa nd na jima banje ba shiyasa bt ba dadewa zamuyi ba ta qarasa mgnr cikin shagwa6a tare da langa6ar da kanta, ok bakomai Allah ya kiyaye hanya cewar Farouk, ta ansa da "amin"
Anan ta ciro 20k ta bashi tace yayi hkr da wannan, ba musu ya kar6a tare dayi mata godiya, ganin ta 6ata rai ne yasa yace "ohhhhh am sorry na daina" suka sakarwa junan su murmushin dake qara fitar masu da kyan su,
Anan sukayi sallama ya wuce, zarah ta dawo seat din mai zaman banxa suka wuce sai gd..... Urs💕Zarah~B~B💕.
😘Fatima~Bello~Bala😘.
AMINAN JUNA
Na💕Xarah~B~B💕
~81-85~
Haba Farouk kaji tsoron Allah wlh kada kaxama sanadin rabuwar way'annan masoya ka tuna fa AMINNAN JUNA ne idan har kuwa kayi qoqarin rabasu to wlh hakkin su bazai barka ba, ka tuna irin son da AMRAH ke maka, kasan bason ta kake ba meyasa zaka yaudare ta?
Farouk ya tashi a fusace yace kaga malam ni ba wa'azi na ne meka ba idan wa'azi kake son kayi kasan inda yadace kaje kayi shi don haka baruwan ka da rayuwata daman dalilin da yasa kaga na fada ma shine don ka fadaman ta yadda zan 6ulluwa lamarin, ba don kaman wa'azi ba yayi tsaki ya fice daga dakin,
Musty kasa aiwatar da komai yayi kallon shi kawai yake yi saki da baki har yabar dakin, yana tunanin irin hali na abokin shi, a fili yake fadin Allah ya shirye mu baki daya"Ni Xarah na ansa da amin"
Washegari!!
Amrah ce tare da Aminiyar ta na hango da alama sun fito daga lectures ne, motar Amrah naga sun nufa suka jingina akan motar, kira naga Amrah tasa har saida ta kusa katsewa sa'annan ya dauka "Hello hubby kai muke jira fa" a dayan bangaren banji me yace ba kawai naji tace ok kayi sauri plz,
Ta juya kallon ta ga Zarah wai yana zuwa, Zarah tace ok bakomai sai yazu...... Urs💕Zarah~B~B💕.
~85-90~
Ba'a dau wani tym ba sai gashi ya isu bayan sun gaisa ne sai Zarah tace "My Amrah ina zuwa plz" ina zaki je ne? Cewar Amrah, ba nisa zanyi ba yanxu zan dawo, Amrah tace ok karfa ki jima, tace insha Allah yanxu zan dawo,
Murmushi kawai Amrah tayi don tasan halin qawar ta sarai bawani gurin zata je ba tayi hakane kawai don ta basu guri ita da hubbyn ta, Shiku Farouk yaji haushin dagawar da tayi bt dole ya danne,
Mota suka shiga Amrah a seat din driver Farouk ana mai zaman banxa bayan sun qare firar su ne ta bashi kudin sa'annan sukayi sallama ya wuce.
BAYAN KWANA BIYU!!
Su Amrah sun fara exams karatu takeyi serious, shiyasa ma yanxu sukan iya 2 days basu hadu da hubbyn ta ba, some tyms saida daddare suke waya mai tsawo,
Zarah ma haka karatu take yi serious, yau ma kamar kullun zarah na room dinta tana karatu qarar wayar ta taji ganin baqowar number yasa taki dagawa, haka akaci gaba da kira bt Zarah ku ajikin ta, taqi daga wayar daga karshe silent ta sakata bcos tana damun ta....Urs💕Zarah~B~B💕.
😘Fatima~Bello~Bala😘
AMINAN JUNA
Na💕Xarah~B~B💕
~71-75~
Zaune suke suna fira cikin jin dadi da farin ciki abin gwanin sha'awa "Dad kaga mun kusa fara exam, Plz dad idan mun qare inson inje katsina nida Zarah gurin Ammi muyi hutun mu acan plz Dad, ta qarashe maganar cikin shagwa6a" Dad yana murmushi yace Amratu kinsan bana son kiyi nesa damu fa, Amrah cikin shagwa6a tace plz dad nafa dade banje ba plz, yace ok Allah ya kaimu tym din, cewar dady suka ansa da "amin" Mum da tunda suka fara mgn kallon su kawai take tana murmushin su na manya, Mum bakice komai ba fa, cewar Amrah, Allah ya kaimu lokacin cewar Mum, Amrah ta ansa da "amin"
Anan Amrah ta bar iyayen nata bayan ta masu saida safe ta wuce room dinta, ta shigarta kuwa Shirin bacci tayi, bayan ta kwanta ne taji qarar wayar ta alamar ana kiran ta, Hubbyn ta, ta gani ya fito kan screen 6aro 6aro, bayan da daga wayar suka gaisa anan kuma suka cigaba da soyewar su, can kuma naji a dayan 6angaren yana fadin "My luv" daman kuma sai yayi shiru, daman me? Cewar Amrah, Plz hubby feel free nd say what ever u want to say plz, daman ina buqatar kudi ne, ajiyar zuciya Amrah tayi sa'annan tace daman wannan ne ka kasa fadaman, ok bakomai kamar nawa kake buqaka?ganin baya da niyar magana yasa tace 20k zasu ishe ka? Cikin rawar murya yace "eh zasu ishe ni my luv" Tnx alot Allah ya saka maki da alkhairi, Amrah ta 6ata rai kamar yana ganin ta tace "No need" kafi karfi komai a wurina hubby insha Allah gobe zan shigo ma dasu......Urs💕Zarah~B~B💕
~75-80~
Am srry na daina cewar Farouk, ok tnx gud nyt Farouk ya ansa da ok swt drm bye bye ta katse wayar.
Har bacci ya suma daukar ta sai taji alamar text ya shigo wayar ta kamar bazata duba ba kuma sai ta duba taga number Hubbyn tace tayi murmushi ta fara karanta wa kamar haka
"Words alone will never be able to express the depth of my luv 4 you".
Gud nyt my luv" Swt drm " Tnx alot once again bye.
Ajiyar zuciya tayi tare da fitar da wani iska huuuuuuuuuuuu sa'annan ta aza wayar akirjinta ta lumshe idonta tare da fadin" I really love u Farouk" ahaka har sarkin barayin ya sace ta.
Bangaren Farouk kuwa murna kawai yakeyi bt acikin zuciyar shi yana tunanin ta ina zai 6ulluwa lamarin don shi har ga Allah bason Amrah yakeyi ba hasalima Aminiyar ta yake so{Ni ku Xarah nace me😳hankalin ka daya kuwa Farouk? Me kake Shirin yi ne? Ganin banida mai ansa man tambayoyina yasa naja baki na😷}
Musty ne ya shigo ganin abokin shi bai masan da shigowarshi ba yasa shi dafa kafadar shi, cikin tsoro Farouk ya juya don ganin waye, ganin musty atsaye yasa shi yin ajiyar xuciya, lafiya kuwa kake Farouk? Cewar musty, yace abokina bazan 6uye maka ba a gaskia ina cikin wata damuwa, musty yace meke damun ka?
Farouk yace musty a gaskia ni bason Amrah nake ba hasalima Aminiyar ta nake so, musty yace wat😳kasan mekake fada kuwa Farouk?.....Urs💕Zarah~B~B💕
😘Fatima~Bello~Bala😘.
AMINAN JUNA
Na 💕Xarah~B~B💕
~61-65~
Ya kalle Musty yace bakomai abokina, are u sure? cewar musty, Farouk ya gyada masa kai alamar"Yes" yace ok Allah yasa muda ce duka suka ansa da "amin".
Washegari!!
Ta kama Monday Amrah ce ta shirya tsaf cikin doguwar riga black, tayi rolling da qaramin gyale mai rabaja red in colour,ta fito ta wuce dinning area acan ta sa me su Dady bayan ta gaishe su, suka fara yin breakfast, soyayyen dankali ne da kawai, da soyayyar doya sai ferfeson kayan ciki, da ruwan tea a flask,
Breakfast sukeyi cikin walwala da ka gansu kasan suna cikin farin ciki, ahaka har suka qare tamasu sallama ta wuce gdn su Zarah.
Ringing biyu ta daga "gani a qofar gd na iso" cewar Amrah, Zarah da sauri2 tama ummah sallama kasancewar yau sun danyi late suka wuce sai UDUS.
Kuda suka isa lecturer har ya shiga da sauri suka nufi hall din suka zauna, bashi da fita ba sai 10 sa'annan wani ya shigo haka suka rinqa yin lectures yau har 4:00pm sa'annan suka kammala.
A kan hanyar kuma warsu ne Amrah ke cewa "My ZARAH" ta juyu da kallon ta ga Amrah tace Na'am ya akayi ne? Amrah tace kinga munkusa fara exam, da munqare inason muje katsina inda qanwar Dadyna, muyi hutun mu acan, inason ki fadawa ummah plz nd nima zan fada mata, Zarah tace Allah ya kaimu nd insha Allah zan fada mata, haka suka ci gaba da firar su har suka isa gd,sukama juna sallama, Zarah bata shiga cikin gd ba sai da taga Amrah ta wuce sa'annan ta shiga.
A parlour ta same Mum tana kallon TV, direct gun Mum ta wuce ta zauna kusa da ita bayan sun gaisa mum tace ya skul din? Amrah ta ansa da lafiya qalau Mum, mun ma kusa fara exam,ok Allah ya taimaka cewar Mum, Amrah ta ansa da "amin" dinning Mum ta nuna mata, tace taje taci abinci, No mum sai nayi wanka tukunna"ok"cewar Mum, daganan ta wuce sai dakinta.... Urs💕Zarah~B~B💕
~65-70~
Da shigar ta, ta nufi bathroom bata jima sosai ba ta fito, bayan ta shirya tsaf cikin qannan kaya riga da skirt ne sun mata kyau sosai sai dan qaramin mayafi da ta dura akanta ta wuce sai dinning area, bayan ta qare ne zata wuce room dinta isuwar dady ne ya hana mata qarasawa "oyoyo dady sannu da zuwa" yauwa Amrah kina lfy? lfy qlw dadyna ya aiki? "Alhamdulillah" cewar Dady, sai a tym din suka gaisa da Mum, tana murmushi tace tahanaka ka huta ta dameka da surutu Amrah ta turo baki Dad yayi dariya yace kyaleta Amratu ta, tayi murmushi sa'annan ta wuce dakinta tabar Mum da Dad nan a parlour,
Tana shiga tayi gun wayar ta, 5 missed call tagani tana dubawa taga 2 missed call na zarar ta ne, sauran kuwa na Farouk ne, ido ta xare sa'annan ta zauna kan gado ta sa kiran Farouk har ta katse ba'a dauka ba ta kara sa kira har ta kusa katsewa sa'annan aka dauka ajiyar zuciya ta fara sauke wa sa'annan tace"Hello hubby shine kaki daukar wayar? Aa bana kusa ne tace ok, nima na bar wayar a dakine ina parlour nida su Mum shiyasa ban daga ba, a dayan banqaren naji yace bakomai my luv, murmushi tayi tare da rungumar pillow" haka suka cigaba da firar su suna zuba soyayyar su,har sukawa juna sallama badun sun gaji da wayar ba.
Sai tym din tasa kiran Zarah bayan sun gaisa, suka ta6a fira kasancewar anfara kiran sallar magreeb yasa basu jima suna wayar ba sukayi sallama.
Toilet ta nufa don dauro alwala bayan ta idar da sallah ta dauko Alqur'an ta fara karanta wa ba ita da tashi ba sai da tayi sallar isha'ee sa'annan ta ninke sallaya da hijab din ta ajiye, Ta wuce parlour anan ta tarar da Mum da Dad da alama dawowar shi kenan daga masallaci....Urs💕Zarah~B~B💕.
AMINAN JUNA
Na 💕Xarah~B~B💕
~51-55~
Yace kamar dai yadda kika sani, suna na "Farouk Adam" ni dan asalin Zamfara state ne, a gusau L/G, acan aka haife ni a shekara ta 25/5/1989 acan nayi karatuna na addini dana boko tun daga primary skul har Scondary skul dina.
Mahaifina Alhaji Adam Muhammad tare da mahayfiya ta Hajiya Baseerah, Auren soyayya sukayi tare da mahaifina, Har Allah ya azurtasu da ya'ya.
Mu biyu ne ga iyayen mu, ni da qanwa ta mai suna Amina, yanxu haka tayi aure harda ya' daya.
Alhamdulillah muna cikin jin dadi da farin ciki duk da mahaifina rufin asiri ne da shi, bayan result dina ya fito ne, na neme admission anan Sokoto state.
Cikin yarda Allah nakuwa samu a nan UDUS, yayin da nake karatun pure chemistry, adan dafe har Allah yanu na man nakai 300 level.
A dai dai wannan lokacin suka iso gurin shan ice cream, anan aka kawo masu ice cream kala kala tun daga vanilla ice cream, strawberry ice cream da dai sauran su.
Anan ne Amrah ta kalle Farouk cike da tausayi, tace hubby na insha Allah daga yau ka fita quncin rayuwa, inason duk tym din da kake da wata buqata ka sanar dani kaji hubby na.
Zarah dake zaune tana sauraron su tun tym din da Farouk ya fara mgn, tayi ajiyar zuciya tare da fadin "Allah yasa muda ce da rabun sa" duka suka ansa da "amin".
Ido suka hada suna wa juna murmushi wanda ke qara fitar da kyan su," Farouk da Amrah kenan " Farouk kyakkyawa ne bt saidai ba fari ne ba wankan tarwada ne wanda turawa ke kira da{Chocalate colour}, aranshi kuwa yana ta ayyana abubuwa daban daban, sai murmushi yake yi wanda da ka ganshi kasan na mugunta ne..........Urs💕Zarah~B~B💕
~55-60~
Lokaci daya suka tashi, suka nufi motar su bayan duk sun shiga, Amrah ta jasu basu tsaya ku ina ba sai a wani babban mall ciki suka shiga gafen boutique suka fara zuwa ta kalle Farouk tace "hubbyna ka zabi kayan da kake so" kallo kawai ya bita da shi, murmushi tamai tace oya dauka mana, anan ya fara za6ar kaya, ganin ya tsaya da ibar kayan yasa ta cigaba da za6ar masa, kaya masu yawa da daukar masa harda shoes ta hadamai da su, daganan suka wuce suma suka za6a ita da zarah komai iri daya suka dauka, haka kayan cosmetic, sunyi sayayya mai yawa, sa'annan suka je Amrah ta biya kudin aka saka kayan a booth suka wuce,
Yinin ranar haka sukayi ta cikin jin dadi da farin ciki sunyi yawo har son gode Allah, sai da yamma suka wuce UDUS suka maida Farouk kasan cewar a hostel yake bayan sun ajiye shi, ya dauki kayan shi dake booth niqi niqi sukayi sallama da shi ya wuce,
Zarah ta dawo seat din mai xaman banxa suka wuce, a hanya Zarah ke cewa Amrah "gaskia kina son Farouk da yawa" Amrah ta kalleta kawai tayi murmushi kamar ba xatayi mgna ba kuma sai tace "Nima haka kawai nake jinshi araina kamar idan ba shi rayuwa ta bazata zama complete ba" Zarah tace to Allah yayi mana za6i mafi alkhairi a rayuwar mu duka suka ansa da "amin" ahaka har suka isa gdn su zarah, "Amrah ta kalle Zarah tace plz ki gaida ummah" Au baxaki shigaba ne cewar Zarah "plz my zarah kiyi hakuri kinga an kusa sallar magreeb kinji" tace ok bakomai ki gaida Mum, ok zataji insha Allah, ahaka suka rabu sunawa juna bye bye.
Da isarta bayan tayi parking ta wuce parlour bata tarar da kuwa ba ta wuce room dinta da shigar ta' ta ajiye hand bag dinta ta wuce toilet wanka ta farayi sa'annan ta dauro alwala ta fito, bayan ta shirya tsaf cikin kaya marar nauyi ta zira dogon hijab dinta don gabatar da sallar magreeb.
Ban garan Zarah kuwa haka ta shiga da kaya niqi niqi a hannun ta, dakin ta ta wuce ta ajiye su, itama toilet ta wuce bayan tafito ta gabatar da sallar magreeb daganan ta wuce da kayan da Amrah ta siya mata room din umman ta, zaune ta same ta kan gado bayan ta gaishe ta, Ta hau nuna mata kayan da Amrah ta siya mata ummah sai murmushin farin ciki take tana qara sawa ya 'yan nata albarka
Zaune yake shi da abokin shi yana nuna mai kayan da Amrar shi ta saya mai bt aranshi yana fadin "Amrah am sorry" maganar da Mustapha keyi wanda suka fi kira da Musty ne ta dawo da shi, yace ya akayi ne aboki na? Farouk ya fitar da iska hade da yin ajiyar zuciya..... Urs💕Zarah~B~B💕.
AMINAN JUNA
Na 💕 Xarah ~ B ~ B
~41-45~
Soyayya mai karfi da shaquwa suka shiga tsakanin Amrah da Farouk, wanda ya kasan ce akuda yaushe idan har suna skul to suna tare, idan kuwa suna gd to fa suna nan maqale da waya.
Yau ta kama Saturday, zaune take tana tunani kala kala aranta,, bude kofar da akayi ne ya maida ta daga duniyar data lula, ganin Aminiyar ta kuma abar kaunar ta yasa ta sakin wani sakaran murmushi wanda ya qara fito mata da kyan ta, itama murmushin ta maida mata,, "My zarah yaushe kika zo cewar Amrah" banjima da zuwa ba Mum tace na duba ki kina daga ciki.
Fira sukayi sosai cike dajin dadin ganin junan su, kusan ranar acan Zarah tayi ni don kuwa ba ita da wucewa ba sai da yamma tayi, sa'annan suka fito ta ma Mum sallama ta wuce.
Haka rayuwa ta kasan ce masu ita da Aminiyar ta kuwanne daga cikinsu baya sun bacin rai daya, soyayya kuwa tsakanin Amrah da Farouk har ba'a mgn domin kuwa Amrah har mmkn irin son da takewa Farouk takeyi.
Kwance yake yana ayyana abubuwa aranshi yana murmushin muganta sai kuma naji yana cewa "Yes" burina ya kusa cika, "ni ku Xarah nace wani burine na Farouk ya kusa cika?" can naga ya dauke wayar shi ya latsa wa, sai naji yana fadin sannunki da hutawa farin idaniya na, wanda ba ku sai anfada ba "AMRAH ce, dayan bangaren akayi mgn bt banji me aka ce ba, sai naji yana fadin da gaske kikeyi" My luv" ok gani nan zuwa,, sai ya katse wayar ya nufi toilet bayan 30m sai gashi ya fito sanye da jalabiya yana goge kanshi da towel din hannun shi,
bayan ya shirya tsaf cikin shadda light blue da hula duk da shaddar ta dan tsufa bt tayi mashi kyau sosai.
A bangaran Amrah kuwa bayan sun qare waya da hubbyn ta, Ta kira Zarah ta fada mata cewa ta shirya zasu unguwa, daga nan toilet ta nufa don yin wanka 30m ta dauka kafin ta fito, Ta wuce gaban madubi don shiryawa........... Urs💕Zarah~B~B💕
~46-50~
Ta kammala shirinta tsaf cikin atamfa brown da digon fari dinkin yayi mata kyau sosai gyalen ta ma fari da dauko hand bag din ta duk ta ajiye akan gado.
Bangaran Farouk kuwa har ya fito ya ciro wayar shi ya kirata domin ta mashi kwatancen area tasu, ringing biyu ta dauka "Hello my luv daga dayan bangaren tace hubby ka iso ne? Yace a'a taya zan iso baki man kwataccen gurin ba, tace au na manta, kasan Sama road? Yace a'a bt zan tambaya ok da ka iso ka kirani kawai yace" ok"
Haka kuwa akayi bai sha wahala sosai ba kasan cewar mashin din da ya daukeshi yasan unguwar, da zuwan shi ya kirata ya shaida mata cewar ya iso.
A palour ta same Mum dinta a zaune kusa da ita ta zauna ta gaida ta, Mum ta ansa fuskar ta dauke da murmushin, Mum ta ce my daughter ina zuwa haka kin kuwa ga yadda kikayi kyau sai kace balaraviya, Amrah ta sunkuyar da kanta tana murmushi Mum gdn su Zarah xanje, Mum tace ok Allah ya tsare hanya my dear, Amrah ta ansa da "Ameen Ameen" ki gaida umman Zarah plz " ok Mum zataji insha Allah" sukayi sallama ta fita.
Motar ta ta nufa bayan sun gaisa da baba mai gadi ya wangale mata gate ta fita, can nesa kadan da gdn su ta hango Farouk yayi matuqar yimata kyau"Aranta tana fadin really Luv my Farouk "a haka har ta isa inda yake bayan sun gaisa ya shiga Motar basu tsaya ku'ina ba sai bakin gdn su zarah.
Ita kuwa zarah tun bayan kare wayar su da Amrah ta same umman ta ta fada mata cewa zasu unguwa da Amrah, Ummah ta amince tare dayi masu fatan alkhairi.
Daga nan zarah ta wuce dakin ta bawani 6ata tym tayi ba ta shirya cikin atamfa green nd white tayi kyau sosai kasan cewar mafi yawancin kayanta duk dadyn Amrah ne ke masu, some tyms ma komai iri daya yake masu.
Bayan Amrah ta gama parking tace da Farouk ina zuwa 2m plz, da fara arta ta shiga gdn bayan sun gaisa da Ummah take tmby ina Zarah? Ummah tace da ita tana ciki, zaune ta same ta tana latsar wayar hannun ta.
Oya my zarah tashi muje yana mota yana jiran mu, Zarah ta xare ido wake jiran mu my Amrah? Amrah tayi murmushin dake qara fito mata da kyan ta, tace hubby na mana, zarah tace au shin da shi za'ayi fitar? Kai kawai Amrah ta gyada mata alamar"eh"tace ok muje,
Anan harabar gdn suka same Ummah tace har kun fito suka ansa da eh tace to Allah ya tsare hanya duka suka ansa da"amin"suka bar gdn rike da hannun junan su,suka nufi motar suka shiga, Zarah a baya, Amrah a driver seat yayin da Farouk yana seat din mai zaman banza.
Driving take ahankali, can sai da kalle Farouk tace "hubby na" ya ansa da na'am my luv tace ina son kabani labarin ka, Farouk ya kalle ta yana murmushi yace ok my luv angama, Ta madubi take kallon Aminiyar ta suka ma junan su murmushi sa'annan ta maida hankalin ta ga Farouk tace "hubby na ina sauraron ka" Farouk wanda shima ita yake kallo ya nisa yace.............Urs💕Zarah~B~B💕