Thursday, 8 December 2016

AMINAN JUNA

        
          
         

            Na 💕 Xarah ~ B ~ B

                         ~41-45~

   Soyayya mai karfi da shaquwa suka shiga tsakanin Amrah da Farouk, wanda ya kasan ce akuda yaushe idan har suna skul to suna tare, idan kuwa suna gd to fa suna nan maqale da waya.

Yau ta kama Saturday, zaune take tana tunani kala kala aranta,, bude kofar da akayi ne ya maida ta daga duniyar data lula, ganin Aminiyar ta kuma abar kaunar ta yasa ta sakin wani sakaran murmushi wanda ya qara fito mata da kyan ta, itama murmushin ta maida mata,, "My zarah yaushe kika zo cewar Amrah" banjima da zuwa ba Mum tace na duba ki kina daga ciki.

Fira sukayi sosai cike dajin dadin ganin junan su, kusan ranar acan Zarah tayi ni don kuwa ba ita da wucewa ba sai da yamma tayi, sa'annan suka fito ta ma Mum sallama ta wuce.

Haka rayuwa ta kasan ce masu ita da Aminiyar ta kuwanne daga cikinsu baya sun bacin rai daya, soyayya kuwa tsakanin Amrah da Farouk har ba'a mgn domin kuwa Amrah har mmkn irin son da takewa Farouk takeyi.

Kwance yake yana ayyana abubuwa aranshi yana murmushin muganta sai kuma naji yana cewa "Yes" burina ya kusa cika, "ni ku Xarah nace wani burine na Farouk ya kusa cika?" can naga ya dauke wayar shi ya latsa wa, sai naji yana fadin sannunki da hutawa farin idaniya na, wanda ba ku sai anfada ba "AMRAH ce, dayan bangaren akayi mgn bt banji me aka ce ba, sai naji yana fadin da gaske kikeyi" My luv" ok gani nan zuwa,, sai ya katse wayar ya nufi toilet bayan 30m sai gashi ya fito sanye da jalabiya yana goge kanshi da towel din hannun shi,

bayan ya shirya tsaf cikin shadda light blue da hula duk da shaddar ta dan tsufa bt tayi mashi kyau sosai.

A bangaran Amrah kuwa bayan sun qare waya da hubbyn ta, Ta kira Zarah ta fada mata cewa ta shirya zasu unguwa, daga nan toilet ta nufa don yin wanka 30m ta dauka kafin ta fito, Ta wuce gaban madubi don shiryawa........... Urs💕Zarah~B~B💕

                          ~46-50~

Ta kammala shirinta tsaf cikin atamfa brown da digon fari dinkin yayi mata kyau sosai gyalen ta ma fari da dauko hand bag din ta duk ta ajiye akan gado.

Bangaran Farouk kuwa har ya fito ya ciro wayar shi ya kirata domin ta mashi kwatancen area tasu, ringing biyu ta dauka "Hello my luv daga dayan bangaren tace hubby ka iso ne? Yace a'a taya zan iso baki man kwataccen gurin ba, tace au na manta, kasan Sama road? Yace a'a bt zan tambaya ok da ka iso ka kirani kawai yace" ok"

Haka kuwa akayi bai sha wahala sosai ba kasan cewar mashin din da ya daukeshi yasan unguwar, da zuwan shi ya kirata ya shaida mata cewar ya iso.

A palour ta same Mum dinta a zaune kusa da ita ta zauna ta gaida ta, Mum ta ansa fuskar ta dauke da murmushin, Mum ta ce my daughter ina zuwa haka kin kuwa ga yadda kikayi kyau sai kace balaraviya, Amrah ta sunkuyar da kanta tana murmushi Mum gdn su Zarah xanje, Mum tace ok Allah ya tsare hanya my dear, Amrah ta ansa da "Ameen Ameen" ki gaida umman Zarah plz " ok Mum zataji insha Allah" sukayi sallama ta fita.

Motar ta ta nufa bayan sun gaisa da baba mai gadi ya wangale mata gate ta fita, can nesa kadan da gdn su ta hango Farouk yayi matuqar yimata kyau"Aranta tana fadin really Luv my Farouk "a haka har ta isa inda yake bayan sun gaisa ya shiga Motar basu tsaya ku'ina ba sai bakin gdn su zarah.

Ita kuwa zarah tun bayan kare wayar su da Amrah ta same umman ta ta fada mata cewa zasu unguwa da Amrah, Ummah ta amince tare dayi masu fatan alkhairi.

Daga nan zarah ta wuce dakin ta bawani 6ata tym tayi ba ta shirya cikin atamfa green nd white tayi kyau sosai kasan cewar mafi yawancin kayanta duk dadyn Amrah ne ke masu, some tyms ma komai iri daya yake masu.

Bayan Amrah ta gama parking tace da Farouk ina zuwa 2m plz, da fara arta ta shiga gdn bayan sun gaisa da Ummah take tmby ina Zarah? Ummah tace da ita tana ciki, zaune ta same ta tana latsar wayar hannun ta.

Oya my zarah tashi muje yana mota yana jiran mu, Zarah ta xare ido wake jiran mu my Amrah? Amrah tayi murmushin dake qara fito mata da kyan ta, tace hubby na mana, zarah tace au shin da shi za'ayi fitar? Kai kawai Amrah ta gyada mata alamar"eh"tace ok muje,

Anan harabar gdn suka same Ummah tace har kun fito suka ansa da eh tace to Allah ya tsare hanya duka suka ansa da"amin"suka bar gdn rike da hannun junan su,suka nufi motar suka shiga, Zarah a baya, Amrah a driver seat yayin da Farouk yana seat din mai zaman banza.

Driving take ahankali, can sai da kalle Farouk tace "hubby na" ya ansa da na'am my luv tace ina son kabani labarin ka, Farouk ya kalle ta yana murmushi yace ok my luv angama, Ta madubi take kallon Aminiyar ta suka ma junan su murmushi sa'annan ta maida hankalin ta ga Farouk tace "hubby na ina sauraron ka" Farouk wanda shima ita yake kallo ya nisa yace.............Urs💕Zarah~B~B💕

No comments:

Post a Comment