Thursday, 8 December 2016

AMINAN JUNA


Na 💕Xarah~B~B💕


                ~51-55~

  
    Yace kamar dai yadda kika sani, suna na "Farouk Adam" ni dan asalin Zamfara state ne, a gusau L/G, acan aka haife ni a shekara ta 25/5/1989 acan nayi karatuna na addini dana boko tun daga primary skul har Scondary skul dina.

Mahaifina Alhaji Adam Muhammad tare da mahayfiya ta Hajiya Baseerah, Auren soyayya sukayi tare da mahaifina, Har Allah ya azurtasu da ya'ya.

Mu biyu ne ga iyayen mu, ni da qanwa ta mai suna Amina, yanxu haka tayi aure harda ya' daya.

Alhamdulillah muna cikin jin dadi da farin ciki duk da mahaifina rufin asiri ne da shi, bayan result dina ya fito ne, na neme admission anan Sokoto state.

Cikin yarda Allah nakuwa samu a nan UDUS, yayin da nake karatun pure chemistry, adan dafe har Allah yanu na man nakai 300 level.

A dai dai wannan lokacin suka iso gurin shan ice cream, anan aka kawo masu ice cream kala kala tun daga vanilla ice cream, strawberry ice cream da dai sauran su.

Anan ne Amrah ta kalle Farouk cike da tausayi, tace hubby na insha Allah daga yau ka fita quncin rayuwa, inason duk tym din da kake da wata buqata ka sanar dani kaji hubby na.

Zarah dake zaune tana sauraron su tun tym din da Farouk ya fara mgn, tayi ajiyar zuciya tare da fadin "Allah yasa muda ce da rabun sa" duka suka ansa da "amin".

Ido suka hada suna wa juna murmushi wanda ke qara fitar da kyan su," Farouk da Amrah kenan " Farouk kyakkyawa ne bt saidai ba fari ne ba wankan tarwada ne wanda turawa ke kira da{Chocalate colour}, aranshi kuwa yana ta ayyana abubuwa daban daban, sai murmushi yake yi wanda da ka ganshi kasan na mugunta ne..........Urs💕Zarah~B~B💕

             ~55-60~

    Lokaci daya suka tashi, suka nufi motar su bayan duk sun shiga, Amrah ta jasu basu tsaya ku ina ba sai a wani babban mall ciki suka shiga gafen boutique suka fara zuwa ta kalle Farouk tace "hubbyna ka zabi kayan da kake so" kallo kawai ya bita da shi, murmushi tamai tace oya dauka mana, anan ya fara za6ar kaya, ganin ya tsaya da ibar kayan yasa ta cigaba da za6ar masa, kaya masu yawa da daukar masa harda shoes ta hadamai da su, daganan suka wuce suma suka za6a ita da zarah komai iri daya suka dauka, haka kayan cosmetic, sunyi sayayya mai yawa, sa'annan suka je Amrah ta biya kudin aka saka kayan a booth suka wuce,

Yinin ranar haka sukayi ta cikin jin dadi da farin ciki sunyi yawo har son gode Allah, sai da yamma suka wuce UDUS suka maida Farouk kasan cewar a hostel yake bayan sun ajiye shi, ya dauki kayan shi dake booth niqi niqi sukayi sallama da shi ya wuce,

Zarah ta dawo seat din mai xaman banxa suka wuce, a hanya Zarah ke cewa Amrah "gaskia kina son Farouk da yawa" Amrah ta kalleta kawai tayi murmushi kamar ba xatayi mgna ba kuma sai tace "Nima haka kawai nake jinshi araina kamar idan ba shi rayuwa ta bazata zama complete ba" Zarah tace to Allah yayi mana za6i mafi alkhairi a rayuwar mu duka suka ansa da "amin" ahaka har suka isa gdn su zarah, "Amrah ta kalle Zarah tace plz ki gaida ummah" Au baxaki shigaba ne cewar Zarah "plz my zarah kiyi hakuri kinga an kusa sallar magreeb kinji" tace ok bakomai ki gaida Mum, ok zataji insha Allah, ahaka suka rabu sunawa juna bye bye.

Da isarta bayan tayi parking ta wuce parlour bata tarar da kuwa ba ta wuce room dinta da shigar ta' ta ajiye hand bag dinta ta wuce toilet wanka ta farayi sa'annan ta dauro alwala ta fito, bayan ta shirya tsaf cikin kaya marar nauyi ta zira dogon hijab dinta don gabatar da sallar magreeb.

Ban garan Zarah kuwa haka ta shiga da kaya niqi niqi a hannun ta, dakin ta ta wuce ta ajiye su, itama toilet ta wuce bayan tafito ta gabatar da sallar magreeb daganan ta wuce da kayan da Amrah ta siya mata room din umman ta, zaune ta same ta kan gado bayan ta gaishe ta, Ta hau nuna mata kayan da Amrah ta siya mata ummah sai murmushin farin ciki take tana qara sawa ya 'yan nata albarka

Zaune yake shi da abokin shi yana nuna mai kayan da Amrar shi ta saya mai bt aranshi yana fadin "Amrah am sorry" maganar da Mustapha keyi wanda suka fi kira da Musty ne ta dawo da shi, yace ya akayi ne aboki na? Farouk ya fitar da iska hade da yin ajiyar zuciya..... Urs💕Zarah~B~B💕.

No comments:

Post a Comment